Resumen del episodio
A Najeriya an cika shekaru goma cur ba tare da an aiwatar da hukuncin kisa ba wanda ya samu sahakewar gwamnati, wadda ita kaɗai ce take ɗaukar matakin ƙarshen wajen aiwatar da hukuncin da kotuna suka yanke dangane da haka. Wannan dai lamari ne da ya sake biijoro da kiraye-kirayen ƙungiyoyin kare haƙƙin ɗan Adam da ke neman a samar da doka da za ta dakatar da aiwatar da hukunci a Najeriya.
A Najeriya an cika shekaru goma cur ba tare da an aiwatar da hukuncin kisa ba wanda ya samu sahakewar gwamnati, wadda ita kaɗai ce take ɗaukar matakin ƙarshen wajen aiwatar da hukuncin da kotuna suka yanke dangane da haka. Wannan dai lamari ne da ya sake biijoro da kiraye-kirayen ƙungiyoyin kare haƙƙin ɗan Adam da ke neman a samar da doka da za ta dakatar da aiwatar da hukunci a Najeriya.
Episodios
Ra'ayoyi: Cikar Najeriya shekaru 10 ba tare da zartas da hukuncin kisa ba
EscuchadoA Najeriya an cika shekaru goma cur ba tare da an aiwatar da hukuncin kisa ba wanda ya samu sahakewar gwamnati, wadda ita kaɗai ce take ɗaukar matakin ƙarshen wajen aiwatar da hukuncin da kotuna suka yanke dangane da haka. Wannan dai lamari ne da ya sake biijoro da kiraye-kirayen ƙungiyoyin kare haƙƙin ɗan Adam da ke neman a samar da doka da za ta dakatar da aiwatar da hukunci a Najeriya.
Ra'ayoyin masu sauraro kan jingine shirin ƙara kuɗin mai a Nijar
EscuchadoMahukuntan Jamhuriyar Nijar sun jingine batun ƙara farashin mai duk da cewa Majalisar Dokokin Riƙon Kwaryar ƙasar ta bayar da shawarar yin wannan ƙari don magance ƙaracin makamashi da ake fama da shi a ƙasar. Wannan na zuwa ne a daidai lokacin da gwamnatin Najeriya ta sanar da wani shirin rage farashin mai a tsawon wata ɗaya domin sauwaƙa wa jama’a. Latsa alamar sauti don sauraren ra'ayoyin jama'a...
Ra'ayoyin masu saurare kan kawo ƙarshen wasa da Argentina da Messi yayi
EscuchadoRa'ayoyin masu saurare kan wasan ƙarshe da Ɗan wasa Lionel Messi ya bugawa ƙasarsa. Ku danna alamar saurare domin jin cikakken shirin tare da Kabiru Muhammad Dan Bauchi.
Ra'ayoyin masu saurare kan fatan ci gaba da haƙo man fetur a wasu sassan arewacin Najeriya
EscuchadoTaron gwamnonin jihohin Arewa maso Gabashin Najeriya da ya gudana a ƙarshen mako, ya buƙaci gwamnatin Bola Ahmed Tinubu ta gaggauta farfaɗo da aikin binciken man fetur da aka faro tsawon shekaru a yankin. Kazalika taron ya buƙaci gwamnatin da ta mayar da hankali wajen gyara layin dogon da ya haɗa biranen Port-court-Jos-Bauchi-Gombe zuwa Maiduguri saboda muhimmancinsa wajen buƙasa tattalin arzikin al’ummar yankin. Ku danna alamar saurare domin jin cikakken shirin tare da Shamsiyya Haruna.
Ra'ayoyin masu sauraro kan ƙarancin makamashi a wasu ƙasashen yammacin Afrika
EscuchadoYayin da kusan a kowane mako ana iya a wayi gari da sabon farashin man fetur a Najeriya, a Jamhuriyar Nijar ana fama da ƙaranci da kuma tsadarsa ne a wasu jihohin ƙasar, yayin da ake fama da gagarumar matsalar ƙarancin gaz da ake amfani da shi domin girki. Ku danna alamar saurare domin jin cikakken shirin tare da Shamsiyya Haruna.